Mahajjaciya ‘yar Najeriya ta rasu a kasar Saudiyya
Daga Sabiu Abdullahi
Wata mahajjaciya ‘yar Najeriya daga jihar Neja mai suna Ramatu Abubakar ta rasu a kasar Saudiyya, kamar yadda hukumar jin dadin alhazai ta jihar ta sanar.
Marigayiyar dai ta rasu ne tana da shekaru 45.
A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar Jibrin Usman Kodo ya fitar, marigayin na daga cikin mahajjatan da suka fara tashi daga filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu zuwa kasar Saudiyya a makon jiya.
Rahmatu, wadda ta fito daga karamar hukumar Bida ta jihar, ta rasu ne a Madina bayan ta yi fama da rashin lafiya a lokacin da ta iso, kuma an kwantar da ita a asibiti inda ta rasu.
Wannan lamari dai wani babban rashi ne ga alhazan jihar Neja, kuma ana ta ta’aziyya ga iyalan mamaciyar.