RASHIN IMANI: An kama yarinyar da ta jagoranci kisar gillar da aka yi wa malamar jami’a
Daga Sabiu Abdullahi
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta damke wata ‘yar aikin gida mai suna Joy Afekafe ‘yar shekara 14 da haihuwa bisa zargin kashe mataimakiyar Farfesa Funmilola Adefolalu ta Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke FUT a Minna a Jihar Neja.
An kama ta ne a unguwar Gbeganu da ke Minna, babban birnin jihar a ranar Litinin bayan binciken share fage na ‘yan sanda.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa wanda ake zargin ta amsa laifin haɗa baki da wasu abokanta maza biyu don aiwatar da kisan.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa yayin da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa ta yi aiki a matsayin yar aikin gidan marigayiyar na tsawon makonni uku amma an sallame ta ne saboda munanan ayyukan da ta yi a gidan.
A cewar sanarwar, “Ta ce bayan an sallame ta, ta haɗu da abokan karatunta da ake kira Walex da Smart, ta ba su labarin irin wahalar da ta sha tare da haɗa baki wajen kai wa malamin hari a gidanta.”
Kakakin ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin ta bayyana cewa, an ɗauke wayar marigayiyar da kwamfutarta, yayin da suka kuma cire batirin motar da ke cikin harabar gidan suka gudu.
Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran waɗanda ake zargin da suka gudu, yayin da za a miƙa wanda ake zargin zuwa hukumar SCID domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su.