October 18, 2025

Trump Zai Sanya Hannu Kan Dokar Da Za Ta Mayar da Ingilishi a Matsayin Harshen Hukuma

images-2025-02-28T215922.828.jpeg

Shugaban Amurka, Donald Trump, na shirin sanya hannu kan wata doka da za ta ayyana turancin Ingilishi a matsayin harshen hukuma a faɗin ƙasar, in ji kafofin yaɗa labarai.

Ko da yake Ingilishi shi ne harshe mafi yawan amfani a Amurka, miliyoyin mutane na magana da wasu harsuna, musamman Sifaniyanci, a gidajensu.

A lokacin yaƙin neman zaɓensa da ya gabata, Trump ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda ake amfani da harsuna daban-daban a ƙasar.

Idan ya sanya wa dokar hannu, Amurka za ta ayyana harshen hukuma a hukumance a matakin tarayya, karo na farko a tarihin ƙasar.

Haka kuma, dokar za ta soke wata doka da aka kafa tun shekarun 1990 a ƙarƙashin tsohon Shugaban ƙasa Bill Clinton, wacce ta bai wa hukumomin tarayya damar tallafawa masu amfani da harsuna da ba Ingilishi ba.