June 14, 2025
IMG-20250228-WA0007.jpg

Daga Salman Isah

Jagorancin Akpabio, a majalisar dattawa ta goma, cike yake da cece-ku-ce da yawaitar suɓul da baka da kuma janyo zazzafar muhawara.

Sanata Godswill Ubot Akpabio jinin PDP ne, yayi gwamnan jihar Akwa Ibom sau biyu kafin zuwa majalisar dattawa bayan da aka zaɓe shi Sanata, kuma a ƙarƙashin mulkin shugaba Goodluck Jonathan, Akpabio ɗan gaban goshi ne, ba ya taɓuwa.

Ya riƙe muƙamai da yawa a zauren majalisa kasancewar sa mutum ne me cika ido (charisma). Kafin ya sauya sheƙa zuwa APC bayan raba gari da tsohon aminin sa kuma shugaban majalisa ta tara, Sanata Abubakar Bukola Saraki, kafin zaɓen 2019.

Duk da kasancewar sa Kirista daga Akwa Ibom, Akpabio ya riga yan Najeriya da dama cin moriyar aƙida da salon siyasar Muslim-muslim, domin an tsara cewa shugaban majalisar dattawa dole zai zama Kirista a wancan lokaci.

Akpabio ya sha kawo cece-ku-ce amma ga fitattu daga ciki:

1. Yace dawo da tsohon taken ƙasa (National Anthem) da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayi, ya nuna tsantsar hangen nesan shugaban domin shi (taken) ne abinda Najeriya ta bi buƙata a lokacin.
2. ⁠Ana tsaka da fama da matsananciyar yunwa da tsadar rayuwa, Akpabio ya kawo sarar ‘Let the Poor Breath’ ma’ana a bar talaka ya numfasa.
3. A watan Agustan 2023, yayin da sanatoci ke tafiya hutu, Akpabio yace ‘ na tura muku addu’oi (kuɗi) don ku sha shagali. Amma ya janye kalaman bayan murza gashin baki daga membobin majalisar.
4. A watan Yulin bara, yayin zaman majalisar, Sanata Natasha daga jihar Kogi ta tashi don tofa albarkacin bakin ta kan wani kudiri, ba tare da ta gabatar da kanta ba kafin fara jawabi, Akpabio yace ta sani ‘majalisa ba gidan nanaye bane’. Makonni biyu bayan haka, Akpabio ya ba ta haƙuri.
5. ⁠A watan Yulin bara yayin da ake dab da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi wa laƙabi da #EndBadGovernance, Akpabio, yayin kira ga matasa da su ƙauracewa shiga zanga-zangar, yace ‘ Duk wanda zai shiga zanga-zanga ya shiga, muna gida muna cika cikin mu’ .
6. Ba zan yi sharhi akan dambarwar sa da Natasha a wannan karo ba domin batu ne dake gaban kotu.

Darussa:

1. Ba a taɓa yin nadamar yinshiru akan maganar da furta ta zai haifar da nadama.

2. ⁠Kada ka tsoma baki a cikin kowane irin zance ko ‘topic’ da ɓullo.

3. ⁠Ka zama mai taƙaita zance, yin haka zai sa ana marmarin zancen ka.

4. ⁠Ba kowane batu za ka yi raha da shi ba, akwai kalaman da ko ka bada haƙuri illar su ba ta gogewa. Dss

Salmanu Isah Darazo
Febrairu 28, 2025.