Tinubu ya gana da tsohon shugaban ƙasa Jonathan a Abuja

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan yadda Najeriya za ta ci gaba da riƙe matsayinta na jagoranci a harkokin dimokuradiyyar Afirka bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar Aso Rock Villa.
Da yake jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin shugabanni na da da na yanzu da kuma masu zabe, Jonathan ya jaddada buƙatar ci gaba a tare, domin samun kyakkyawar makoma.
Da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, Jonathan ya bayyana yadda aka kammala zabe da kuma wajibcin samun haɗin gwiwa wajen tunkarar ƙalubalen tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce, “Zabuka sun ƙare, don haka dole ne mu ci gaba…Eh, muna da ƙalubale a fannin tattalin arziki a yanzu, amma har yanzu muna da abin da ake bukata don jagorantar Afirka.”
Jonathan, wanda aka san shi da rawar da yake takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da difulomasiyya a faɗin nahiyar, ya bayyana irin rawar da zai taka a tattaunawar yankin.
Ya bayyana shirinsa na ziyartar ƙasashen Kenya da Laberiya, da nufin ba da gudummawa ga kokarin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yammacin Afirka da ma Afirka baki ɗaya.
Ganawarsa da shugaba Tinubu ta zo daidai da hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen watan Fabrairu, ya ba wa Jonathan damar taya shugaban kasa murnar nasarar da ya samu.
I coul not refrainn ftom commenting. Well written!
Wow, awesome bllg format! Howw lengthy hazve you everr been runnning a blog for?
yoou made bloggying glaance easy. The overall lokok of your sitye is magnificent, ass neatly as
tthe contrent material!
If you want too obtai a grrat deall fropm this aryicle then you hve
too applyy such techniques too our won blog.