October 18, 2025

Shugaba Tinubu Ya Jagoranci Taron Ƙusoshin Jam’iyyar APC a Fadar Shugaban Kasa

FB_IMG_1740517889490.jpg

Daga The Citizen Reports

Shugaban kasa Bola Tinubu yana jagorantar taron kwamitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Aso Rock.

Wannan taro, wanda manyan jiga-jigan jam’iyyar suka halarta, shi ne na farko tun bayan da Tinubu ya hau mulki a watan Mayu na shekarar 2023.

Taron na zuwa ne gabanin zaman kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na APC da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

A bisa al’ada, mambobin jam’iyyar APC, ciki har da gwamnoninta, kan gudanar da taron kwamitin kafin zaman NEC.

Daga cikin wadanda suka halarta akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje.

Haka nan, dukkan gwamnonin da suka samu nasara a karkashin jam’iyyar APC sun halarci taron.