May 17, 2025

Mummunar Gobara Ta Tashi a Kasuwannin Ladipo da Owode Onirin a Legas

images-2025-02-25T211600.123.jpeg

Gobara ta tashi a shahararrun kasuwannin Ladipo da ke Mushin da Owode Onirin da ke kan titin Ikorodu a Legas, inda ta haddasa asarar miliyoyin naira.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta fara ne da tsakar daren Talata, inda ta bazu cikin shaguna da rumbunan ajiyar kaya. An bayyana cewa kayan da suka ƙone sun haɗa da injuna, kayayyakin gyaran motoci da babura, da kuma na’urorin lantarki na gida.

Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Margaret Adeseye, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce jami’an agajin gaggawa daga cibiyoyin kashe gobara na Isolo, Bolade, da Alausa sun hanzarta zuwa wurin domin shawo kan wutar, duk da ƙalubalen da suka fuskanta wajen isa yankunan.

A lokaci guda, wata gobara ta sake tashi a kasuwar Owode Onirin, inda ta ƙone shaguna da dama masu sayar da kayan ƙarafa. Jami’an kwana-kwana daga Alausa da Ikorodu sun isa wurin domin kashe wutar.

Adeseye ta tabbatar da cewa ba a samu asarar rayuka ba a gobarar biyu, kuma ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin tashinsu.

1 thought on “Mummunar Gobara Ta Tashi a Kasuwannin Ladipo da Owode Onirin a Legas

Comments are closed.