Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or a karo na takwas

Daga Sabiu Abdullahi
Kyaftin din Argentina Lionel Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or karo na takwas.
Messi dai ya zama gwarzon ɗan ƙwallon duniya ne a ranar Litinin a birnin Paris na kasar Faransa.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa Messi ya doke gwarzon dan wasan ƙwallon kafa na Turai UEFA na bana, da kuma ɗan wasan Manchester City Erling Haaland.
Kylian Mbappe na Faransa da Paris St Germain ya shiga jerin sunayen manyan ‘yan wasa uku a duniya.