Kisan Gaza Na Firgitar Da Ni—Guardiola

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa yana cikin “firgici sosai” saboda yadda ake ci gaba da kisan jama’a a Zirin Gaza, sakamakon yaki tsakanin Isra’ila da mayaƙan Hamas.
Tun bayan harin ramuwar gayya da Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023, inda aka kashe aƙalla mutane 1,200 kuma aka sace wasu 251, Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza a matsayin martani ita ma.
Kimanin wata 20 kenan, rahoton Ma’aikatar Lafiya ta Gaza wadda ke ƙarƙashin Hamas ya nuna cewa aƙalla Falasɗinawa 54,800 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren Isra’ila.
Guardiola, wanda ya fito daga Barcelona a ƙasar Sifaniya, ya bayyana damuwarsa cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, yana cewa: “Abin da muke gani a Gaza abu ne mai ƙona zuciya. Yana ƙona jikina baki ɗaya.”
Ya ci gaba da cewa: “Bari na bayyana ƙarara – wannan ba magana ba ce ta aƙida ko siyasa. Magana ce ta girmama rayukan ɗan’adam da jin kai ga maƙwabta. Ko da mu na ganin yaran da aka kashe a asibiti ba mu jin komai, ya kamata mu fahimta cewa wata rana hakan na iya faruwa da namu.”
Guardiola ya ce tun lokacin da rikicin ya fara, kullum yana kallo ‘ya’yansa Maria, Marius da Valentina, yana jin tsoro da damuwa.
Ba sabon abu ba ne ga Guardiola bayyana ra’ayinsa a kan batutuwan siyasa.
A baya, hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta ci shi tara saboda saka rigar da ke nuna goyon baya ga ‘yan Catalonia masu fafutukar neman ‘yanci daga Sifaniya.