October 18, 2025

Gwamnatin Zamfara ta sake rufe kasuwannin da take zargin ana amfani da su wajen sayar da shanun sata

images-2023-12-17T184343.950.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin jihar Zamfara ta sake rufe kasuwannin shanu 11 a wasu sassan jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Munnir Haidar, ya ce an sanar da rufe kasuwannin ne saboda rahotannin tsaro cewa ‘yan fashi suna amfani da kasuwannin wajen sayar da shanun da suka sato.

Kasuwannin da abin ya shafa, a cewar Haidar, su ne Kasuwannin Tsafe da Bilbis da ke karamar hukumar Tsafe, Kasuwar Jangebe da ke karamar hukumar Talata-Mafara, da Kasuwar Wuya da ke karamar hukumar Anka.

Sauran su ne kasuwar Magamin Diddi da ke karamar hukumar Maradun, kasuwar Galadi da ke karamar hukumar Shinkafi, da Kasuwar Mada da ke karamar hukumar Gusau, da Sabon Birnin Danali a karamar hukumar Birnin Magaji.

Sai kuma kasuwannin Kokiya, Chigama, da Nasarawar Godel, duk a karamar hukumar Birnin Magaji.

Ya ce gwamnatin jihar ta umurci jami’an tsaro da su tabbatar da bin doka da kame duk wani mutum da ya saba wa umarnin.