January 14, 2025

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu.

0
Oluwarotimi-Akeredolu.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Rahotanni na nuna cewa Gwamnan Indo Rotimi Akeredolu ya rasu yana da shekaru 67 a duniya a yau Laraba a birnin Lagos.

An tattaro cewa likitocin fadar gwamnatin jihar ne suka lura da shi har zuwa rasuwarsa saboda ba za su iya kai shi kasar waje ba.

“Akeredolu ya mutu; Ya rasu ne a Legas,” wata majiya mai tushe ta shaida wa wata jaridar a Najeriya.

Ku tuna cewa gwamnan, a lokacin da yake jinya, ya dawo Najeriya a watan Satumba bayan shafe watanni uku a Jamus.

Kwanan nan, ya sake komawa hutun jinya bayan da shugaba Bola Tinubu ya umarce shi da ya mika mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *