October 18, 2025

Gwamnatin Tinubu na shirin fara cire wa mutanen da ke samun miliyan 100 harajin kaso 20 a kowane wata

IMG-20241014-WA0003.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin Najeriya ta gabatar da sabon kudirin haraji da zai kara yawan harajin kudin shiga da mutane masu hannu da shuni za su bayar.

A cewar Taiwo Oyedele, Shugaban Kwamitin Manufofin Kudi da Sauye-Sauyen Haraji na Shugaban Ƙasa, wadanda ke samun Naira miliyan 100 ko fiye a kowane wata za su rika ba da harajin kashi 25%.

Oyedele ya bayyana wannan a taron tattalin arzikin Najeriya karo na 30 a Abuja a ranar Litinin.

Ya bayyana bukatar da ke akwai na daidaita lissafi, inda ya ce, “Idan kana samun naira miliyan 100 a wata, za mu dauki kashi 25 daga cikin kuɗaɗen.”

Sauye-sauyen da aka gabatar sun yi nufin ware masu karamin karfi daga biyan harajin kudin shigar, tare da rage wa masu karamin karfi da ke samun Naira miliyan 1.5 ko kasa da haka a wata nauyin haraji.


Ana sa ran sauye-sauyen harajin da aka gabatar za su fara aiki daga watan Janairu 2025, muddin majalisar dokoki ta amince da kudirin.

3 thoughts on “Gwamnatin Tinubu na shirin fara cire wa mutanen da ke samun miliyan 100 harajin kaso 20 a kowane wata

  1. Today, I went to the beachfront with mmy children. I
    found a sea shell andd gave itt too mmy 4 yearr oldd daughter annd
    szid “You can hear the ocean if you put this to your ear.” She put
    thee shell too her eaar and screamed. Thre was a hermit
    crab inside and it pinchrd herr ear. Shhe nevcer wants too go
    back! LoL I kno thios iss completely off topic but I haad
    to twll someone!

Comments are closed.