April 19, 2025

Amurka ta ce za ta daina ba wa Izraa’eela tallafin makamai idan ta ci gaba da…

FB_IMG_1729021161467.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Amurka ta aike wa gwamnatin Isra’ila wasiƙa, inda ta ba ta wa’adin kwana 30 don ta ƙara yawan kayan agajin da ake kai wa Gaza, ko kuma ta fuskanci katsewar tallafin makamai da Amurka ke ba ta.

A cewar wasu rahotannin, wasiƙar dai ita ce mafi tsauri da gwamnatin Biden ta taɓa aikewa Isra’ila tun bayan barkewar yaƙin Gaza shekara guda da ta gabata.

Takardar, wadda aka aika kwanaki biyu da suka wuce, tana ɗauke da sa-hannun sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, da sakataren tsaro, Lloyd Austin.

A cikin wasiƙar, sun bayyana damuwa kan tabarbarewar yanayin al’amuran jinƙai a Gaza.

Saƙon ya kuma bayyana cewa a watan da ya gabata, Isra’ila ta ki amincewa ko kuma ta katse kaso 90 na ayyukan jinƙai a arewacin Gaza.

A ƙarshe, wasiƙar ta ba wa Isra’ila wa’adin wata guda na “daukar matakan gaggawa don magance matsalar.”

“Dole ne Isra’ila ta fara ɗaukar kwararan matakai daga yanzu har zuwa kwana 30 don bai wa kayan agaji damar shiga,” in ji wasiƙar, tare da ƙara da cewa gazawa wajen yin hakan zai shafi tsare-tsaren Amurka.

108 thoughts on “Amurka ta ce za ta daina ba wa Izraa’eela tallafin makamai idan ta ci gaba da…

  1. Wondsrful ggoods from you, man. I’ve consider your stff prior to aand you’re just extremely fantastic.

    I actually lik what youu have bught right here, reall like what youu aare stating andd
    thee bet wayy throughh which youu ssay it. You are mking
    iit entertaining andd youu still care ffor to stay
    itt smart. I can not waitt tto read much mopre from you.
    That is reallly a remendous web site.

  2. вывод из запоя на дому краснодар круглосуточно [url=https://uaforum.ukrbb.net/viewtopic.php?f=13&t=3235]вывод из запоя на дому краснодар круглосуточно[/url] .

Comments are closed.