Gwamnan Neja ya ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N80,000 ga ma’aikatan jihar

Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya amince da N80,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati a jihar.
Wannan matsaya ta samu ne yayin wata ganawa da aka yi da wakilan ƙungiyoyin ma’aikata a Minna, babban birnin jihar Neja, a ranar Juma’a.
Gwamna Bago ya bayyana amincewa da sabon mafi karancin albashin.
Rahotanni sun ambato gwamnan yana cewa, “A matsayinmu na gwamnatin jiha, mun yanke shawarar amincewa da mafi karancin albashi na N80,000 (Naira Dubu Tamanin).”
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan sanarwar da wasu gwamnoni suka yi a jihohinsu. Idan ba a manta ba, Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya sanar da sabon mafi karancin albashi na N80,000 ga ma’aikatan jihar a ranar Laraba tare da ƙirƙirar kwamitin mutum 15 domin kula da aiwatar da shi.
Shi ma Nasir Idris, gwamnan jihar Kebbi, ya amince da N75,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan jiharsa.
Gwamna Bago ya bayyana cewa yana da kudurin aiwatar da sabon mafi karancin albashi da sauran shirye-shiryen jin daɗin ma’aikata a jihar.
Haka kuma, gwamnan ya gode wa dukkan ma’aikatan jihar bisa hakuri da fahimtar da suka nuna duk da matsalolin tattalin arziƙi da tsaro da ake fuskanta.