January 16, 2026

Gwamnan Neja ya hana ma’aikatan gwamnatin jihar zuwa ofis da babbar riga ko kaftani

images-2023-12-18T171354.974.jpeg

Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya bayyana cewa ya fitar da sabuwar dokar inda ya hana ma’aikatan gwamanti zuwa ofis da kaftani ko babbar riga.

BBC Hausa ta rawaito cewa dokar za ta fara “aiki ne daga yau Litinin a duk faɗin jihar inda ya danganta dalilinsa da cewa ‘aiki aka je yi ba saka kaftani ba’.”

Ya ce, “Babu ma’aikacin gwamnati da zai sake saka kaftani ko babbar riga ya je aiki a Neja. Duk wanda ke son saka kaftani, sai dai ya bar aikin.”

Ya zuwa yanzu dai, bankaɗe-bankaɗen TCR Hausa bai gano wasu ƙwararan dalillai da suka sa aka sanya wannan doka wa ma’aikatan gwamantin jihar ba.