Tashin farashin kayayyaki ya tilasta wa mutanen Neja fitowa zanga-zanga

Daga Sabiu Abdullahi
Mazauna Minna, babban birnin jihar Neja, sun cika kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da tsadar abinci da rayuwa da ake fama da su a faɗin Najeriya.
Daruruwan masu zanga-zangar sun tare hanyar Minna zuwa Bida a babbar unguwar Kpakungu da misalin karfe 7 na safiyar ranar Litinin.
Ƙoƙarin da ‘yan sanda suka yi na shawo kan jama’a ya kusan haifar da tashin hankali yayin da masu zanga-zangar suka nemi ‘yan sanda da su fice, lamarin da ya tilasta wa ‘yan sanda harbin bindiga.
Ƴan Najeriya dai na ta fama da mummunan tashin farashin kusan komai da ake amfani da shi a ƙasar, kama daga man fetur har zuwa kayan abinci.