October 18, 2025

Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Ba Wa Sani Danja Muƙami a Gwamnatinsa

images-2024-12-16T055413.439.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada shahararren jarumi daga masana’antar Kannywood, Sani Musa Danja, a matsayin mai bashi shawara ta musamman kan harkokin matasa da wasanni.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, an bayyana cewa nadin ya fara aiki nan take.

Baya ga wannan, gwamnan ya amince da karin nade-nade, inda ya nada Dr. Ibrahim Musa a matsayin mai kula da lafiyarsa kuma mashawarci kan sha’anin lafiya.

Ga jerin sauran nade-naden da aka yi:

Dr. Hadiza Lawan Ahmad – Mai Ba da Shawara na Musamman kan Zuba Jari da Hadin Gwiwa Tsakanin Gwamnati da Masana’antu.

Barr. Aminu Hussain – Mai Ba da Shawara na Musamman kan Shari’a da Al’amuran Kundin Tsarin Mulki.

Dr. Ismail Lawan Suleiman – Mai Ba da Shawara na Musamman kan Yawan Al’umma.

Nasiru Isa Jarma – Mai Ba da Shawara na Musamman kan Kungiyoyi na Gida.

Hon. Wada Ibrahim Daho – Kwamishina na Daya, Hukumar SUBEB.

Hon. Ado Danjummai Wudil – Sakatare Janar, Hukumar Koyar da Shawara.

Dr. Binta Abubakar – Sakatare Janar, Hukumar Ilimi na Jama’a.

Hon. Abubakar Ahmad Bichi – Darakta Janar, Hukumar Kula da Kananan Harkokin Kasuwanci da Sana’o’in Tituna.

Hon. Abdullahi Yaryasa – Memba, Hukumar Kula da Harkokin Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Dr. Yusuf Ya’u Gambo – Shugaban Hukumar Kula da Tsarin Mulki da Tsare-Tsare.

16 thoughts on “Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Ba Wa Sani Danja Muƙami a Gwamnatinsa

Comments are closed.