Sojojin Najeriya Sun Kama Shugaban ‘Yan Bindiga Da Ake Zargi Yana Da Hannu a Kisan Sarkin Gobir
Daga Sabiu Abdullahi
Dakarun rundunar sojojin Najeriya ta 1 Brigade sun kama wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga kuma dillalin makamai, Bako Wurgi, wanda aka fi sani da Baka NaGarba.
Wurgi na cikin wadanda ake zargi da sacewa da kisan Sarkin Gobir, Isa Mohammad Bawa, a Jihar Sakkwato.
Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, ya bayyana a shafinsa na X cewa an gudanar da samamen da ya kai ga cafke Wurgi ranar Asabar, 14 ga Disamba, 2024.
A cewarsa, bayanan sirri sun nuna cewa Wurgi yana samun kulawa a wani asibiti a garin Shinkafi, Jihar Zamfara, sakamakon raunuka da ya samu a wata arangama da wata kungiyar ‘yan bindiga.
Makama ya ce, “Bayanan sirri sun tabbatar min cewa dakarun sojoji sun kama Wurgi bayan gano cewa an kai shi asibiti domin kula da raunuka na wuƙa da harbin bindiga.”
A yayin samamen, wasu daga cikin abokan aikinsa guda biyu sun tsere, amma sojojin sun kama wani mutum da ya taimaka wajen jigilar Wurgi a babur mai kafa uku.
Idan ba a manta ba, an yi garkuwa da marigayi Sarkin Gobir ranar 9 ga Yuli, 2024, a karamar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato, inda aka kashe shi ranar 22 ga Agusta bayan tattaunawar sakinsa ta gaza cimma nasara.
A cewar Makama, “Rahotanni sun nuna cewa Wurgi ya taka muhimmiyar rawa a sacewar da kuma kisan, wanda suka hada da tattaunawar fansa da ta kunshi kudi da babura, amma hakan bai yi nasara ba.”




