April 18, 2025

ECOWAS Ta Ba Wa Mali, Burkina Faso, da Nijar Watanni 6 Don Sake Shawara Kan Ficewa Da Kungiyar

FB_IMG_1734322616147.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta bai wa kasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar wa’adin watanni shida don su sake tunanin shawarar da suka yanke na ficewa daga kungiyar.

Shugaban Hukumar ECOWAS, Dakta Omar Touray, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a birnin Abuja, bayan zaman taron shugabannin kasashen kungiyar karo na 66.

A cewarsa, “Shugabannin kasashen ECOWAS sun karɓi sanarwar da aka samu daga Jamhuriyar Burkina Faso, Mali, da Nijar game da shawarar da suka yanke na ficewa daga ECOWAS.”

Ya kara da cewa kasashen uku za su daina zama membobin ECOWAS daga ranar 29 ga Janairu, 2025, bisa tanadin sashe na 91 na sabon kundin tsarin ECOWAS.

Wa’adin watanni shida, daga Janairu 29 zuwa Yuli 29, 2025, na nufin ba kasashen uku damar sake duba matsayinsu, tare da ci gaba da bude kofa don dawowarsu kungiyar.

A wannan lokacin, shugabannin kasashen Togo da Senegal za su ci gaba da kokarinsu na shiga tsakani don dawo da kasashen uku cikin ECOWAS.

Shugabannin ECOWAS sun yaba wa kokarin diplomasiyyar Shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal, Shugaba Faure Gnassingbé na Togo, da Shugaban kungiyar ECOWAS, Shugaba Bola Tinubu.

A jawabin karshe, Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin hadin kai da karfin zuciya wajen magance matsalolin da ke addabar yankin. Ya ce, “Yayin da muke tunkarar aiwatar da kudurorin wannan taro, mu kasance tsintsiya madaurinki daya wajen tabbatar da akidar da ke hada mu a matsayin al’umma daya.”