#EdoDecides2024: Gwamna Obaseki ya ce PDP ce za ta lashe zaɓen jihar in dai babu wanda ya yi magudi

Daga Sabiu Abdullahi
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kada kuri’arsa a makarantar firamare ta Emokpa da ke unguwar Oredo Ward 4, Rumfa ta 19, da misalin karfe 11:55 na safe a yayin da ake gudanar da zaben gwamna.
Da yake bayyana babu hayaniya a wajen zaɓen zuwa wannan lokacin, Obaseki ya bayyana fatansa na ganin jam’iyyarsa ta samu nasara.
“Ina da yakinin dan takarar jam’iyyarmu zai lashe zaben idan ba a yi magudin zabe ba,” inji shi.
Gwamnan ya kara da cewa, “Daga rahoton da muke samu tun daga lokacin ya nuna cewa ana gudanar da zaɓen cikin lumana, ba mu samu wani mummunan labari ba kawo yanzu.”
A halin da ake ciki, dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Olumide Akpata, shi ma ya bayyana gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben.
Bayan ya kada kuri’arsa a rumfar zabe mai lamba 11, Ward 6 a karamar hukumar Oredo da misalin karfe 10:30 na safe, Akpata ya bayyana fatan ganin an gudanar da zaɓen cikin lumana a fadin jihar.
Ya yi kira da a bar magoya bayansa su kada kuri’unsu ba tare da cikas ba.
Duk da ruwan sama da aka fara yi da misalin karfe 10 na safe, jama’a sun fito da dama, inda suka nuna aniyarsu ta shiga harkokin zaben.
أنابيب الصلب المجلفن في العراق تُعرف مصنع إيليت بايب كواحدة من أفضل وأكثر الشركات المصنعة لأنابيب الصلب المجلفن موثوقية في العراق. تُنتج أنابيب الصلب المجلفن لدينا بدقة ومعايير عالية الجودة، مما يضمن المتانة ومقاومة التآكل. هذه الأنابيب مثالية لمجموعة متنوعة من التطبيقات، بما في ذلك إمدادات المياه، والبناء، والاستخدامات الصناعية. بفضل مرافقنا الحديثة والتزامنا بالتميز، أنشأت مصنع إيليت بايب سمعة قوية في تقديم منتجات عالية الجودة تلبي احتياجات عملائنا بفعالية. اكتشف المزيد عن أنابيب الصلب المجلفن لدينا بزيارة موقعنا الإلكتروني على ElitePipe Iraq.