January 14, 2025

Jami’in gidan gyaran hali ya kashe abokinsa a Bauchi

0
FB_IMG_1726827525533

Daga Sabiu Abdullahi   

Wani lamari ya faru a gidan gyaran hali na Burra da ke jihar Bauchi, inda ake zargin wani jami’in gyaran gidan gyaran hali ya kashe abokin aikinsa bisa rashin jituwa da suka samu a kan abinci.  

Shugaban karamar hukumar Ningi, Hon. Nasiru Zakari, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis.  

Ya ce, “Na samu rahoto game da wannan abin takaicin da ya faru a gidan gyaran hali na Burra, inda ake zargin wani jami’i ya kashe abokin aikinsa saboda rashin jituwa kan abincin rana.”  

A cewar Ahmad Usman Tata, jami’in hulda da jama’a na hukumar gidan gyaran hali ta jihar Bauchi, lamarin ya faru ne a wajen gidan gyaran hali.  

Ya bayyana cewa marigayin, Aliyu Abubakar Chiroma, ya fito ne daga karamar hukumar Giade, yayin da wanda ake zargin Kabiru Abubakar ya fito daga karamar hukumar Dass.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fara ne a lokacin da Chiroma ya kawo abincin rana, kuma Kabiru ya dage sai ya ci, lamarin da ya janyo cece-ku-ce a tsakanin su biyun.  

Tuni dai aka mika gawar marigayin ga iyalansa domin yi masa jana’iza, yayin da wanda ake zargin yake hannun ‘yan sanda don ci gaba da gudanar da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *