DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu ya rattaba hannu kan sabon kudirin gyara mafi karancin albashi na N70k a matsayin doka

Daga Sabiu Abdullahi
Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan sabon kudirin gyara mafi karancin albashi na kasa na shekarar 2024, inda ya kayyade mafi karancin albashi na N70,000.
Za a riƙa sake duba dokar duk bayan shekaru uku.
An gudanar da bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin, kwanaki kadan bayan majalisar dokokin kasar ta amince da kudirin.
Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin a tsakiyar taron majalisar zartarwa ta tarayya.
A cewar shugaban ma’aikatan, “babu shakka sabuwar dokar za ta tabbatar wa ma’aikata cewa shugaban ya damu da walwalarsu.”
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya jagoranci shugabannin Majalisar kasar zuwa wurin rattaba hannun, inda Shugaba Tinubu ya godewa Majalisar Dokoki ta kasa kan hanzarta amincewa da dokar.