January 15, 2025

DA DUMI-DUMI: An fara zanga-zanga a Jihar Neja

26
images-6-15.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Matasa a jihar Neja sun fito kan tituna domin nuna adawa da tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya, inda suka yi ta buga kwalaye masu dauke da sakonni irin su ‘Ya isa’ da kuma ‘Dakatar da Manufofin Yaki da Talakawa’.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki ne ta hanyar Abuja zuwa Kaduna a karamar hukumar Suleja, inda suke rera wakokin nuna rashin jin dadinsu.

Zanga-zangar na nuna rashin gamsuwar da ‘yan kasar ke samu kan manufofin tattalin arziki da suke ganin na kara lalata yanayin rayuwarsu.

Bukatun dawo da tallafin man fetur na nuna irin matsalar kudi da da yawa ke fuskanta.

Omoyele Sowore, mai rajin #RevolutionNow, ya fitar da jerin bukatu 15 daga ‘yan Najeriya zuwa ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Bukatun sun hada da soke kundin tsarin mulkin kasar na 1999, da biyan ma’aikatan Najeriya mafi karancin albashi na Naira 250,000 duk wata, da kuma saka jari mai tsoka a fannin ilimi.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya nemi a ba shi lokaci domin tabbatar da lamarin amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai mayar da martani ba.

26 thoughts on “DA DUMI-DUMI: An fara zanga-zanga a Jihar Neja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *