January 14, 2025

Kisar Najeebah: Tinubu ya sha apwashin shawo kan matsalar tsaro

13
IMG-20240112-WA0038.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin magance matsalar sace-sace da hare-haren ‘yan bindiga a kasar nan.

Tinubu, wanda ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake fama da su, ya bayyana su a matsayin abin tayar da hankali, rashin tsoron Allah, da kuma mugun nufi.

Shugaban ya yi wannan alkawari ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Jam’iyyatu Ansaridden ta Harkar Musulunci a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Talata.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman Cif Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Talata.

A kwanakin baya ne wasu ‘yan bindiga suka kashe wata budurwa mai suna Najeebah da suka yi garkuwa da ita da wasu ‘yan uwa mata guda biyar a Abuja.

A ranar 9 ga watan Janairu ne aka sace Najeebah da yayyenta tare da mahaifinsu.

Daga bisani ‘yan bindigar sun saki mahaifin nasu, inda suka bukaci ya je ya nemo naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa don a sako ‘ya’yansa mata kafin Juma’a 12 ga watan Janairu.

Amma ‘yan bindigar sun kashe ta, suka aika da gawarta ga iyayenta bayan sun kasa samun kudin fansar da ake bukata.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce tana kara kaimi wajen ceto wadanda abin ya shafa.

13 thoughts on “Kisar Najeebah: Tinubu ya sha apwashin shawo kan matsalar tsaro

  1. Woah! I’m really digging the template/theme off this
    website. It’s simple, yett effective. A loot off timess it’s
    challenging to get that “perfect balance” betaeen user friendliness and appearance.
    I must ssay you’ve done a fantastic job withh this. Additionally, thee boog loads super fast foor mee onn Opera.
    Excellen Blog!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *