October 18, 2025

Borno: Tubabbun mayakan BH sun tsere da makamai da baburan da gwamnati ta ba su

images-14-19.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Akalla tubabbun mayakan Boko Haram 13 sun tsere da manyan makamai da babura da gwamnatin jihar Borno ta ba su.

A cewar jaridar Premium Times, ana koyar da mayakan tare da ba su kayan yaƙi domin su shiga cikin sojojin Najeriya don yaƙi da ‘yan ta’adda.

Gwamnatin Borno ta bayyana cewa ta samu nasarar sake shigar da tubabbun mayakan Boko Haram guda 8,490 cikin al’umma ta hanyar tsarin Borno Model.

Amma sabbin bincike sun nuna cewa mayakan da aka haɗa da sojojin a Mafa sun tsere tsakanin ranar 1 zuwa 2 ga watan Satumba, 2024.

Daya daga cikin waɗanda suka tsere, Abdullahi Ishaq, ya yi barazanar haddasa fitina a jihar.

Masanin bincike, Malik Samuel, ya nuna cewa wannan lamarin ya saka alamomin tambaya kan tsarin sake shigar da tubabbun mayakan ciki al’umma.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2021, wasu daga cikin tubabbun ‘yan Boko Haram sun yi barazanar komawa cikin ƙungiyar idan gwamnati ta kasa cika musu alkawuransu.

Wannan na faruwa ne duk da ƙarancin ayyukan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar.

4 thoughts on “Borno: Tubabbun mayakan BH sun tsere da makamai da baburan da gwamnati ta ba su

Comments are closed.