January 14, 2025

Kais ya sake zama Shugaban Tunisiya

1
IMG-20241009-WA0021.jpg

Daga Sodiqat A’isha Umar

Shugaban ƙasar Tunisiya Kais Saied ya samu nasarar lashe zaɓe karo na biyu da gagrumar nasara, inda ya lashe sama da kashi 90 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana.

Zaɓen wanda ya sha suka wajen ƙungiyoyin kare haƙki, ƴan takara biyu kaɗai cikin goma sha biyu aka ba ba damar tsayawa takara da shugaba Saied, yayin da kashi 29 cikin 100 na mutane sama da miliyan tara da suka yi rajista suka kaɗa ƙudu’a.

Babu wani kamfen da ƴan takarar suka yi, kuma kusan dukkan fastocin da aka liƙa bisa tituna na goyon bayan shugaban ƙasar ne.

An yi hasashen cewa Saied zai samu gagarumar nasarar tun bayan da hukumomi suka kama tare da ɗaure wasu manyan abokan hamayyarsa, ciki har da biyu daga cikin ƴan takarar shugabancin ƙasar.

1 thought on “Kais ya sake zama Shugaban Tunisiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *