Ba Za Mu Daina Kai Hari Kan Isra’ila Ba, Za Mu Faɗaɗa Hare-Hare Har Zuwa Sansanonin Sojin Amurka—Iran

Iran ta bayyana cewa ba za ta dakatar da hare-haren da take kai wa Isra’ila ba, inda ta ƙara da cewa za ta faɗaɗa su zuwa sansanonin sojin Amurka da ke yankin a cikin kwanaki masu zuwa.
Wannan na zuwa ne a matsayin martani kan hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan cibiyoyin da Iran ke da su.
Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya ruwaito cewa Iran ta na da niyyar ci gaba da kai farmaki har sai Isra’ila ta nuna nadama bisa hare-haren da ta fara kai wa.
Wani babban jami’in gwamnatin Iran ya shaida wa kafafen watsa labarai cewa, “arangama ba za ta tsaya a abin da ya faru daren Jumma’a kawai ba.”
A nata bangare, tashar talabijin ta Iran ta bayar da rahoton cewa fiye da mutane 60 ne suka rasa rayukansu, ciki har da yara 20, a wani mummunan hari da Isra’ila ta kai kan unguwar gidaje a babban birnin ƙasar, Tehran.
A wani hari dabam da Isra’ila ta kai a yammacin Iran, mutum biyu ne suka mutu a wurin ajiye makamai masu linzami da ke garin Assadabad.
Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa mafi yawan makaman da Iran ta harba cikin Isra’ila an cafke su da taimakon kawayen Isra’ila, sai dai wasu kalilan ne suka faɗo har suka haddasa barna a Tel Aviv.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta yi amfani da jiragen yaƙi da kuma jiragen leƙen asiri marasa matuka wajen kai wani babban hari cikin ƙasar Iran.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 78, yayin da fiye da 320 suka jikkata.Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya mayar da martani ga Iran inda ya gargadi jagoran juyin juya halin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.
Ya ce: “Za mu kona Tehran ƙurmus idan har Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami kan fararen hula a Isra’ila.”
A halin da ake ciki, ƙasashen biyu na ci gaba da kai wa juna hari, inda kowanne bangare ke amfani da garkuwar kare sararin samaniyarsa don dakile hare-haren da ake kai masa.
Iran ta sake kai wani harin ramuwar gayya da safiyar Asabar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku tare da jikkatar wasu da dama.
Halin da ake ciki yanzu ya janyo fargaba a tsakanin al’ummomin duniya, yayin da ake kara jin tsoron cewa tashin hankali na iya yaduwa zuwa wasu sassa na Gabas ta Tsakiya.