January 24, 2025

Hatsarin jirgin sama ya yi ajalin Shugaban Iran Ebrahim Raisi

0
IMG-20240520-WA0003.jpg

Daga Sodiqat Aisha Umar

Jami’an Iran sun ce Shugaba Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar, Hossein Amir-Abdollahian sun rasu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a wani yanki da ke kusa da kan iyaka da Azerbaijan.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an ga tarkacen jirgin a tsakanin wasu tsaunuka.

Shugaban ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran, Pirhossein Koolivand ya ce masu aikin ceto sun nufi wurin tarkacen jirgin amma babu alamar akwai waɗanda suka tsira.

JIrgin saman mai saukar ungulu na ɗauke ne da shugaba Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar Hossein Amir Abdollahian.

Sauran waɗanda suke cikin jirgin sun haɗa da Ayatollah Mohammad Ali Al-e Hashem – limamin masallacin Juma’a na birnin Tabriz da Janar Malek Rahmati watau gwamnan lardin gabashin Azerbaijan.

Kwamandan askarawan kare lafiyar shugaban ƙasa, Sardar Seyed Mehdi Mousavi, da waɗansu jami’an tsaron na cikin waɗanda suka yi hatsari a jirgin mai saukar angulu.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani jami’in gwamnatin Iran na cewa jirgin ‘ya kone ƙurmus’.

Jirgin saman mai saukar ungulu ya faɗi ne a wani yanki mai tsaunuka mai nisa sosai kuma da farko aikin ceto shugaban ƙasar ya gamu da cikas sakamakon rashin kyawun yanayi da hazo.

Tun farko jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei ya yi kira ga mutanen da su yi wa dukkanin wadanda ke cikin jirgin addu’a.

Kawo yanzu ba a san musabbabin haɗarin jirgin sama mai saukar ungulun ba amma ɓangaren sufurun jirgin saman Iran ya fuskanci koma baya sakamakon takunkuman da Amurka ta sanya kasar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *