December 7, 2025

Iran ta kai hari Isra’ila a karon farko

AFP__20220909__32HY7LM__v1__HighRes__IranDefenceDrill-1713040843.jpg

Daga Muhsin Ibrahim

A karon farko, Iran ta harba jiragen yaƙi marasa matuƙi kusan guda 50 zuwa ga Isra’ila. Hakan ya biyo bayan wani mummunan hari da Isra’ila ta kai kan ofishin jakadancin Iran da ke Damascus, Syria. Yanzu ana zaman ɗar-ɗar a Isra’ila, saboda sai nan da wasu awanni jiragen za su isa.

Amurka da ma Isra’ila sun ce sun shirya tsaf don kakkaɓo jiragen gaba ɗaya. Tuni dama Amurka ta tura da manyan jiragen ruwanta na yaƙi yankin ta tsakiya. Sannan sojojinta da suke Jordan da Saudiyya su ma sun shirya domin kare Isra’ila.

Wannan dambarwar za ta iya jawo yaƙin duniya na uku. Iran ba kanwar lasa ba ce. Sannan tana da ƙawayen da za su iya taimaka mata, ko ma su shigar mata idan ta kama. Ana kuma tsoron suna da makaman ƙare dangi (nuclear weapons).

Isra’ila kuwa ba a ce wa komai. Amurka da ƴan koronta (kamar yadda suka saba) da ma ita kanta Isra’ila a shirye suke da kowane irin yaƙi. Suna da nuclear weapons kuma.

Muna addu’ar Allah ya tsagaita wannan bala’in, amin. Allah ya ba wa mai gaskiya nasara, amin.