October 18, 2025

Ba mu da wani shirin haɗewa da PDP, in ji LP

ATIKU-AND-OBI.jpg

Jam’iyyar Labour a ranar Alhamis ta ce ba ta da wani shiri na haɗewa da jam’iyyar PDP domin rusa APC jam’iyya mai mulki a babban zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.

Dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Talata, ya ba da shawarar cewa jam’iyyun adawa su haɗa kai domin kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen shugaban kasa mai zuwa.

Kakakin LP, Obiora Ifoh yayin da yake mayar da martani ga shawarar Atiku a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis ya ce jam’iyyar ba ta tattauna batun hadewar ba.

Ifoh ya ce kiran da Atiku ya yi “shawara ce kawai kuma kowane dan Najeriya ya kamata ya yi sha’awar ganin dimokuradiyya ta yi aiki a Najeriya kuma abin da muke da shi a halin yanzu shi ne kama karya”.

66 thoughts on “Ba mu da wani shirin haɗewa da PDP, in ji LP

Comments are closed.