January 14, 2025

Kotu ta tabbatar da Fubara na jam’iyyar PDP a matsayin halattaccen gwamnan jihar Ribas

0
Collage-Maker-02-Jun-2023-09-18-PM-3093-1024x597-1.webp

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a jihar Legas a ranar Talata, ta yi watsi da karar da Tonye-Cole na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya shigar da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara na jam’iyyar PDP.

Tonye-Cole ya bukaci Kotun Ɗaukaka Ƙara ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a watan Maris.

Ya shaida wa kotun cewa Fubara yana ci gaba da sanya hannu a kan takardu a matsayin Akanta-Janar na Jihar ko da bayan an tsayar da shi a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP.

Ya kuma yi zargin an tafka kura-kurai a zaben.

A watan Oktoba ne kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Rivers ta yi watsi da karar, inda ta ce jam’iyyar APC da ta dauki nauyin Tonye-Cole ta janye karar da aka shigar kan nasarar da Fubara ya samu.

Daga nan ne Tonye-Cole, wanda bai gamsu da hukuncin kotun ba, ya tunkari Kotun Ɗaukaka Ƙara domin neman hakkinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *