January 15, 2025

Wasu fusatattun matasa sun jefi gwamnan Benue

7
Alia-1024x577.webp

Daga Sabiu Abdullahi

Wasu matasa sun kai hari kan ayarin motocin gwamnan jihar Benue, Rev Fr Hyacinth Alia, a unguwar Ugondu da ke karamar hukumar Makurdi ta jihar a ranar Laraba.

Matasan na unguwar Ugondu da ke karamar hukumar Makurdi ta jihar Binuwai, wadanda suka yi wa ayarin gwamnan da duwatsu, sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da shirin binne mamallakin kwalejin Vaatia, Makurdi, Engr. Michael Vaatia a cikin harabar makarantar da ke cikin unguwarsu.

Rahotanni sun nuna cewa shida daga cikin matasan da suka yi zanga-zangar ‘yan sanda sun kama su da laifin jefa abubuwa kan ayarin motocin gwamnan.

Gwamna Alia ya ziyarci Kwalejin Vaatia ne domin tantance matakin da aka shirya na binne mamacin.

Engr Vaatia, wanda shi ne shugaban Kwalejin, ya rasu kwanaki biyu da suka gabata kuma za a binne shi a harabar makarantar ranar Alhamis.

7 thoughts on “Wasu fusatattun matasa sun jefi gwamnan Benue

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *