October 18, 2025

Ba mu biya ko sisi don sakin ƴan bautar ƙasa da aka yi garkuwa da su ba—NYSC

images-2023-12-14T195759.521.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar matasa masu yi wa kasa hidima ta NYSC ta ce ba ta biya kudin fansa domin ganin an sako wasu ƴan bautar ƙasa da aka sace a jihar Zamfara.

A wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC, Eddy Megwa, a ranar Alhamis, hukumar ta lura cewa an sako hudu daga cikin ‘yan kungiyar 8 da aka sace ya zuwa yanzu, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na NYSC.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Har ila yau, abin lura ne a bayyana cewa, babu wata gwamnati ko wata hukuma da ta biya wani kudi da sunan kudin fansa kafin a sake su.

“Hukumomin masu yi wa kasa hidima, tun bayan da aka sako su, suna daukar nauyin kudaden jinyarsu inda suke samun sauki.

“Don haka hukumar ta nesanta kanta da ikirarin cewa gwamnatin jihar Akwa Ibom ko wata gwamnatin jihar ta biya kudi domin a sake su.”

5 thoughts on “Ba mu biya ko sisi don sakin ƴan bautar ƙasa da aka yi garkuwa da su ba—NYSC

  1. Ищете надежного сантехника в Минске? Мы проводим чистку и обслуживание с высоким качеством. Наши квалифицированные сантехники готовы осуществить замену. Узнайте больше на установка унитаза минск .

Comments are closed.