October 18, 2025

An kama ƴan luwaɗi sama da 50 a Gombe

images-2023-10-23T103032.468.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC), reshen jihar Gombe, ta dakile shirin auren jinsi daya, wanda ya kai ga cafke mutane 76.

An dai kama wadanda ake zargin ne a filin Duwa Plaza da ke kan hanyar Bauchi zuwa Gombe, inda waɗanda ake zargin suka taru domin bikin zagayowar ranar haihuwar ‘yan luwadi da aka yi da nufin yin bikin auren jinsi.

Buhari Sa’ad, jami’in hulɗa da jama’a na jihar, ya bayyana cewa, a cikin waɗanda aka kama, akwai maza 59, yayin da 21 suka amsa cewa ‘yan luwadi ne.

Bugu da ƙari, an kama mata 17 a wurin. An gabatar da waɗanda ake zargin a gaban ‘yan jarida a hedikwatar rundunar da ke Gombe, ƙarƙashin kulawar kwamandan jihar, Mohammed Muazu.

“Za a gurfanar da su gaban kotu domin amsa laifin da suka aikata abin da ya shafi zamantakewa, wanda laifi ne a jihar Gombe,” in ji Sa’ad.