An fara rabon kayan tallafi a Abuja
Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta fara rabon buhunan shinkafa da masara 12,000 ga magidanta masu ƙaramin karfi a fadin kananan hukumomi shida na babban birnin tarayya Abuja.
A ranar Litinin ne aka fara rabon kayayyakin abincin da aka shirya gudanarwa na tsawon kwanaki biyu a kananan hukumomin Kwali, Kuje, da Abaji.
Da yake magana a madadin ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a garin Kwali, sakataren ma’aikatan karamar hukumar, Bitrus Garki ya bayyana cewa shirin, wani ɓangare ne na rabon kayan agajin da hukumar ta FCTA ke rabawa mazauna yankunan.
Ya ce kowace karamar hukumar za ta samu buhunan shinkafa da masara da bai yi ƙasa da 2000 ba.
Garki ya ce: “Za ku iya tuna cewa kimanin makonni biyu da suka gabata, hukumar babban birnin tarayya Abuja ta shirya wani taron inda aka raba wasu kayan abinci ga ƙungiyoyi daban-daban.
“Wannan ya haɗa da ƙananan hukumomi, wakilan sarakuna 17, kungiyoyin addini, ma’aikatan gwamnati, da kuma ƙungiyoyin masu rauni.”
Відгуки про Мостбет свідчать про високий рівень довіри серед користувачів | Mostbet online – це зручність та надійність в одній платформі mostbet официальный сайт. | Мостбет онлайн – ваш вибір для якісного відпочинку та виграшів | Завантажте додаток Мостбет та насолоджуйтесь азартом будь-де [url=https://mostbetcasinouahfgy.com/]Мостбет UA[/url].