Asusun Laminu na Duniya ya yaba wa gwamnatin Najeriya saboda cire tallafin mai
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yaba da matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na cire tallafin mai a taron shekara-shekara na bankin duniya da IMF da ke gudana a birnin Marrakesh na kasar Morocco.
Duk da haka, IMF ta nuna wajibcin aiwatar da tsare-tsare don rage wa ƴan kasa talakawa tsananin rayuwa.
Mataimakin Daraktan Sashen Kudi na IMF, Era Dabla-Norris, ta yi jawabi ga manema labarai bayan wani zama mai taken ‘Fiscal Monitor.
Ta jaddada mahimmancin rage wa al’umma masu rauni tsadar rayuwa.
Ƴan Najeriya dai har yanzu na ta kokawa saboda ƙuncin tattalin arziki musamman tun bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.