An hallaka dakarunmu 8 a artabu da Heböllähi—Izra’ilah

Daga Sabiu Abdullahi
Isra’ila ta sanar da cewa an kashe sojojinta takwas a Lebanon yayin da har yanzu dakarunta ke fafatawa da mayaƙan Hezbollah a ƙasa.
A baya-bayan nan, rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa sojojinta sun yi arangama da ƙungiyar Hezbollah.
Isra’ila ta tura ƙarin sojoji zuwa kan iyakarsu da Lebanon don yaƙar Hezbollah.
Haka kuma, Isra’ila ta yi gargaɗi ga ƙauyuka 20 a kudancin Lebanon da su fice daga gidajensu, tare da nanata gargaɗin bayan fara faɗa a ƙasa.
Hukumomin lafiya a Lebanon sun ce an kashe mutane 55 a wasu sassan ƙasar a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama a ranar Talata.
Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da mutuwar wani babban kwamandanta.
A hannu guda, Hezbollah ta ba da rahoton arangama da sojojin Isra’ila a aƙalla garuruwa biyu da ke kan iyaka, tare da bayyana cewa za ta kori dakarun Isra’ila daga yankin.
A wajen wani taro na masu ruwa da tsaki a Iran, shugaban addinin ƙasar ya bayyana cewa domin a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, ƙasashen yammacin duniya dole ne su fice daga yankin.