January 14, 2025

Kungiyar Hizbullah ta kai hare-hare ta sama kan sansanonin sojojin Isra’ila

240
images-2023-10-24T170610.591.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar a jiya Alhamis cewa ta kai hare-hare da dama kan sansanonin sojojin Isra’ila.

Hare-haren dai martani ne ga yaƙin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin kungiyar Hizbullah da sojojin Isra’ila a kan iyakar Isra’ila da Lebanon tun bayan fara yaƙin tsakanin kungiyar Hamas ta Falasdinu da Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

Kungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran ta bayyana cewa mayaƙanta sun aiwatar da hare-hare sau 19 a lokaci guda kan sansanin sojojin Isra’ila ta hanyar amfani da makamai masu linzami, manyan bindigogi, da sauran makamai.

Wasu bama-bamai guda biyu sun kai hari a wani sansanin sojojin Isra’ila a yankin gonakin Shebaa da ke kan iyaka da ake taƙaddama a kai.

Sai dai Kamfanin Dillancin Labarai na Labanon ya ruwaito cewa, mutane 4 sun rasa rayukansu a kusa da kauyen Hula da ke kudancin kasar a lokacin da Isra’ila ta kai musu hari.

Ban da wannan kuma, hare-haren da Isra’ilan ta kai kan yankuna daban-daban a kudancin kasar Lebanon da ke kan iyakar kasar sun janyo hasarar rayuka da jikkatar fararen hula.

Tsananin hare-haren da aka kai da harsasai ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba, lamarin da ya bar mazauna yankin cikin fargaba da damuwa.

Rikicin ya kuma haifar da ci faruwar abubuwa a siyasa, yayin da shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah ke shirin gabatar da jawabinsa na farko tun bayan yakin.

Har yanzu dai al’amura sun taɓarɓare, inda ɓangarorin biyu suka yi musayar wuta da juna, lamarin da ya ƙara ta’azzara halin da ake ciki a yankin.

240 thoughts on “Kungiyar Hizbullah ta kai hare-hare ta sama kan sansanonin sojojin Isra’ila

  1. купить диплом о среднем образовании в кирове [url=https://man-diploms.ru/]купить диплом о среднем образовании в кирове[/url] .

  2. где можно купить диплом о высшем образовании [url=https://orik-diploms.ru/]где можно купить диплом о высшем образовании[/url] .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *