Hezbollah ta ce nan ba da jimawa ba za ta sanar da sabon shugabanta
Daga Sabiu Abdullahi
Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta faɗa a ranar Litinin cewa za ta zabi sabon shugaban da zai maye gurbin Hassan Nasrallah da aka kashe, tare da ci gaba da yakin da take yi da Isra’ila tun shekaru da dama.
Mataimakin shugaban kungiyar, Naim Kassem, a cikin wani jawabi da aka yi ta talabijin, ya ce za a zabi sabon shugaba da zai karbi mukamin sakatare janar din maye gurbin Nasrallah nan da nan.
Ya ce tsarin kungiyar ya ba su damar samun maye gurbin dukkan manyan shugabanni, kasancewar suna da mataimaka da mambobin da suka cancanta.
“Mun san cewa fafatawar na iya daukar lokaci mai tsawo, kuma mun shirya don duk wata mai yiwuwa. Idan Isra’ila ta yanke shawarar kaddamar da harin kasa, mu ma mun shirya domin yakar su a fili.”
Al’amura a Gabar ta Tsakiya dai na ƙara rincaɓewa musamman tsakanin Isra’ila da Falasdinu da Lebanon da Iran.