AFCON: Gwamnatin Kaduna ta ɗauki nauyin nuna wasan ƙarshe tsakanin Najeriya da Kwaddibuwa

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ɗauki nauyin nuna wasan ƙarshe da Nigeria za ta fafata da ƙasar Ivory Coast a yau ɗin nan a wasu muhimman wurare a faɗin jihar.
Kamar yadda bayanai suka bayyana, za a nuna wasan ne a Jamiar Ahmadu Bello Zaria, Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zaria da kuma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya ta Kaduna.
Haka nan kuma za a nuna wasan a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya da kuma Jami’ar Jiha ta Kaduna.