October 18, 2025

Sojoji 17 Sun Gamu Da Ajalinsu Yayin Arangama da ‘Yan Ta’adda a Neja

images - 2025-04-11T060501.455

Akalla sojojin Najeriya 17 ne suka rasa rayukansu yayin wata arangama mai tsanani da ‘yan ta’adda a garin Bangi da ke ƙaramar hukumar Mariga a Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne cikin daren ranar 24 ga Yunin 2025, yayin da dakarun sojin ƙasa tare da haɗin gwiwar sojin sama suka yi yunkurin dakile shirin wasu ‘yan ta’adda fiye da 300 da ke ƙoƙarin shigowa garin ta dajin Kwanar Dutse zuwa dajin Kwatankoro.

A cewar sanarwar da daraktar watsa labarai na rundunar sojin ƙasa, Laftanal Kanal Appolonia Anele, ta fitar, an gano cewa ‘yan ta’addan na shirin kai hare-hare ne a wasu ƙauyukan da ke makwabtaka da yankin ko kuma suna ƙoƙarin tserewa daga hare-haren da ake kai musu a jihar Zamfara.

Sojojin ƙasa sun yi arangama da ‘yan ta’addan na tsawon sa’o’i uku cikin dare, kafin rundunar sojin sama ta shiga cikin al’amari ta hanyar kai farmaki daga sama, wanda ya tilasta ‘yan ta’addan janyewa cikin rudani.

Sanarwar ta ce: “Jinin ‘yan ta’adda da dama da aka gani a hanyoyin da suka bi yayin gudu na nuna cewa sun yi babban rashi.”

Sai dai, har yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda suka mutu daga cikinsu ba. Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da tsaftace yankin daga sauran ‘yan ta’addan da suka tsere.

Rundunar sojin ta bayyana cewa, a yayin artabun, sojoji 17 sun mutu, inda wasu 10 kuma suka samu raunuka.

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin soji, kuma an tabbatar da cewa suna samun kulawa cikin gaggawa.Babban hafsan sojin ƙasa, Laftana Janar Oluwafemi Oluyede, ya bayyana jimaminsa dangane da rashin da aka yi na jaruman sojin.

Ya ce: “Sadaukarwar da suka yi don kare kasar nan ba za a taɓa mantawa da ita ba.”

Ya kuma tabbatar da cewa an ɗauki duk matakan da suka dace don kula da lafiyar waɗanda suka jikkata.

Haka kuma, Janar Oluyede ya umarci rundunonin da su ba iyalan waɗanda suka mutu cikakken tallafi, tare da yabawa jarumtaka da ƙwazon dakarun.

A nata jawabin, kakakin rundunar sojin Najeriya ta ce: “Sojin Najeriya ba za su ja da baya ba wajen kare rayuka, tsaron al’umma da tabbatar da hadin kan kasa.”

Ta kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanan sirri domin taimaka wa yaki da ta’addanci.qaq