October 18, 2025

Ƴan majalisa na ƙoƙarin tsige Gwamna Fubara

Collage-Maker-02-Jun-2023-09-18-PM-3093-1024x597.webp

Daga Sabiu Abdullahi

Majalisar dokokin jihar Ribas ta fara shirin tsige gwamnan jihar, Siminialayi Fubara.

Don haka ne ‘yan majalisar dokokin jihar suka aika da sanarwar tsige Fubara bayan tsige shugaban majalisar, Edison Ehie, wanda ake kyautata zaton yana bangaren gwamnan.

Mambobi 24 cikin 32 na Majalisar Ribas sun sanya hannu kan takardar tsige Fubara.

An dai dauki matakin ne a zaman gaggawa da ‘yan majalisar suka yi a safiyar ranar Litinin.

Zaman da ba a saba gani ba ya gudana ne tsakanin karfe 7 na safe zuwa karfe 9 na safiyar ranar Litinin.