October 18, 2025

Yadda matasa a Jihar Yobe ke ƙoƙarin yi wa ‘yan majalisu 3 kiranye

IMG-20240207-WA0001(1)

Daga Sabiu Abdullahi  

Al’ummar mazaɓar yankin Yobe ta Kudu a Jihar Yobe sun shigar da kokensu gaban Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a Abuja, inda suka bukaci a yi kiranye ga ‘yan majalisa guda uku. 

Shafin farko na takardar koken ke nan

‘Yan majalisar sun haɗa da Sanata Ibrahim Mohammed Bomoi, Honourable Fatima S. Talba, da Honorabul Ahmed Adamu.   

Masu shigar da koken, waɗanda suka bayyana kansu a matsayin “masu kaɗa kuri’a/masu zabe”, sun bayyana cewa ba su aminta da wakilcin ‘yan majalisar uku ba, “saboda rashin kulawa da kuma watsi da al’ummominsu.”   

“Muna jin cewa mambobin da aka ce namu ne sun yi watsi da mu, ba tare da kai tsaye sun nuna alamun kasancewarsu tare da al’ummominmu ba. Hakan ya bayyana mana cewa kuri’unmu kawai suke so bayan sun bar mu a wani hali,” in ji masu koken.   

Takardar koken ta bayyana irin munanan yanayi da mazauna yankin ke fuskanta, da suka haɗa da yunwa, fatara, da karuwar mace-macen yara saboda rashin samun kulawar lafiya da abinci.   

Masu zaɓen sun jaddada buƙatar tasu cikin gaggawa, inda suka ce, “Don haka, wajibcin wannan koke na nuni da cewa mun yanke shawarar janye su daga majalisun dokokin ƙasa da na jihohi.”   

Wani dan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma Darakta Janar na Atiku The Light Organisation ne ya wallafa koken a shafukan sada zumunta a ranar Laraba.