October 18, 2025

Yadda ake cika takardar neman bashin da gwamnati za ta ba wa ɗalibai

images-4-18.jpeg

Daga Abdullahi I. Adam

Hukumar bada lamuni ga ɗalibai ta Najeriya, NELFUND, a jiya Juma’a, ta buɗe shafinta na yanar gizo domin soma karɓar takardun neman lamuni ga ɗaliban makarantun gwamnatin tarayya zango na farko.

Shafin hukumar wanda ya soma aiki a jiya Juma’a, zai fara karɓar bayanan ɗaliban makarantun gwamnatin tarayya kaɗai kamar yadda babban jami’in hukumar mai kula da labarai da hulɗa da jama’a, Nasir Ayitogo, ya bayyana.

Kamar yadda babban jami’in hukumar ya fayyace, cike bayanan ya ƙunshi matakai ne daki-daki kamar haka:

Buɗe shafin bayanai ga mai neman lamuni

Mataki na 1: a shiga www.nelf.gov.ng

Mataki na 2: a latsa “Apply Now”

Mataki na 3: a latsa “Get Started”

Mataki na 4: za’a amsa wasu tambayoyi sannan idan za’a cigaba a danna “Yes I am Nigerian”

Mataki na 5: ɗalibi zai sanya bayanai na makarantar da yake tare da tabbatar da cewa makarantar ta miƙa bayanansa waɗanda suka haɗa da lambarsa ta rajista.

Mataki na 6: a nufi daidai inda aka rubuta “Verify with JAMB” sai a saka bayanan JAMB

(Ɗaliban da ba su shigar da NIN ɗinsu lokacin JAMB ba, za su ga inda za su shigar da NIN ɗin don tantancewa)

Mataki na 7: ɗalibi zai buɗe shafin bayan shigar da bayanan email nasa sai a danna “Create Account”

Mataki na 8: sai ya ɗalibi ya shiga email ɗinsa don amincewa da saƙon da zai amsa na neman buɗe shafi

Idan an kammala wannan abinda ya rage shi ne cike bayanan neman lamunin kamar haka:

Za’a danna “Log in” sai a cike bayanai da suka ƙunshi:

Mataki na 1: shigar da email da password

Mataki na 2: a latsa “Proceed to Contact Details”

Mataki na 3: za’a shigar da cikakkun bayanan adireshi, kamar lambar waya, adireshin gida, jiha da kuma ƙaramar hukuma.

Mataki na 4: shigar da cikakkun bayanan makarantar da ake karatu sai a latsa “Proceed to Account Details”

Mataki na 5: shigar da bayanan BVN, sunan banki da kuma lambar asusun banki. In an shigar sai a latsa “Save Changes”

Cike bayanan irin bashin da ake buƙata

Mataki na 1: a latsa “Request for Student Loan”

Mataki na 2: a nan ɗalibi zai zaɓi irin bashin da yake nema tsakanin “upkeep loan” ko “institutional charge” sai ya cika

Mataki na 3: za’a saka takardar shiga makaranta. sai kuma ID card ko rasiɗi na biyan ƙuɗi in an ga dama

Kafin cigaba, tilas a karanta ƙa’idoji da dokokin bashin sai a cigaba.

Mataki na 4: za’a karanta gamsassun bayanai game da bashin sai a latsa “Submit Application”

Mataki na 5: a latsa “Loans” don sanin halin da ake ciki game da neman lamunin.

Wannan rance da za’a riƙa ba ɗalibai an so a soma shi tun watan Oktoba na shekarar 2023 sai dai an jinkirta shi zuwa watan Afrilu na bana ne domin ƙara shiryawa.