October 18, 2025

Tinubu ya nemi Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar Atiku

Tinubu-and-Atiku.png

Suleiman Mohammed B.

Shugaba Tinubu ya bayyana roƙonsa a gaban Kotun Ƙoli don yin watsi da daukaka ƙara da PDP ta yi.

A cewar shugaban, hakan da tamkar raina shari’a ne da hukuncin da kotun baya ta zartar, ya yi kuma addu’ar a kori ƙarar gaba daya, inda ya kara tabbatar da sahihancin nasararsa.

Shugaba Tinubu ya yi kakkausar suka kan cewa Atiku da PDP sun kasa tabbatar da ikirarin da suka yi akan nasarar zaɓensa kotu .

Ya dage sosai da cewa hukuncin da Kotun ta yanke na tabbatar da zabensa na sahihi ne.

Ya kuma roki Kotun Ƙoli da ta tabbatar da hukuncin da karamar kotun ta yanke tare da yin watsi da daukaka karar gaba dayansa, saboda rashin cancanta da kuma niyya ta gaskiya.


Da farko Atiku Abubakar da PDP sun shigar da kara ne domin nuna adawa da sakamakon zaɓen shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Daga cikin korafe-korafen da suka yi, masu shigar da kara sun yi zargin cewa an tafka kura-kurai da kuma rashin bin dokar zabe.

Sun kuma yi zargin cewa Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, ba su cancanci tsayawa takara ba, kuma ba su samu nasara ta hanyar mafi rinjayen kuri’un da aka kaɗa ba.

Sai dai kotun sauraren ƙararrakin zaben shugaban kasa, a hukuncin da ta yanke ranar 6 ga watan Satumba, ta yanke hukunci kan Atiku, inda ta ce ya kasa tabbatar da zargin da yake yi a ƙarar da ya shigar.

Ba tare da ɓata lokaci ba, Atiku ya shigar da kara a gaban kotun koli a ranar 18 ga Satumba, 2023.