January 13, 2025

Mazauna Potiskum sun koka bayan shafe rabin shekara ba tare da wutar lantarki ba

318
images-2023-10-12T091405.765.jpeg

Daga Suleiman Mohammed B.

Waddansu mazauna Ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jihar Yobe sun nuna damuwarsu ƙarara a kan halin da suke ciki na rashin wutar lantarƙi sanadiyar lalacewar ‘gidan wuta’ wato na’urar da take ƙara musu ƙarfin wuta.

Aƙalla yau kimanin watanni shida ke nan suna fama da matsalar wutar lantarki a cikin unguwarsu Daɗin Kowa, a gundumar Dogonini da ke Potiskum.

Sun tabbatar wa manema labarai irin baƘar wahalar da suka sha na rashin ruwa, niƙa da dai sauran muhimman abubuwan more rayuwa da sai da wutan lantarƙi suke aiki.

Wannan ya zamo wani ƙalubale ne mussaman ga ƴan siyasar yankin Ƙaramar Hukumar Potiskum wadda take shiyyar Yobe to ƙudu, lura da mazaɓar Dogonini ta fi kowanne kowacce mazaɓa ba da kuri’u masu ɗinbin yawa a shiyyar, saboda ɗandazon Al’ummar da suke da shi a wannan yankin.

Sun shaida cewa duk wata hanya da za a bi don su samar wa unguwarsu injin wuta sun yi amma har yanzu shiru.

A cewar al’ummar, har Damaturu, hedkwatar jihar, sun kai ƙorafinsu gaban wakilansu na siyasa amma har yanzu abin ya ci tura.

Don haka suna ƙira ga shuwagabanni da masu faɗa-a-ji da su dubi irin halin da ake ciki su kai kukansu gaba don a magance musu matsalar da ta addabesu kimanin watanni da dama.

318 thoughts on “Mazauna Potiskum sun koka bayan shafe rabin shekara ba tare da wutar lantarki ba

  1. Купить тепловизоры FLIR серии ONE, TG, EX и С от официального дилера. Бесплатная доставка по всей стране. 2 года официальной гарантии. Заходите!

  2. Купить тепловизор для наблюдения и охоты Grand Pulsar Официальная гарантия 3 года Доставка по Украине Pulsar, Infiray(Iray), Hikvision, Pard Цена от 700$.

  3. I am curious to find out what blog platform you’re utilizing?

    I’m having some small security problems with my latest blog and I
    would like to find something more risk-free. Do you have any suggestions?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *