Tinubu ya nemi ƴan ƙasa su dage da yin addu’a yayin da tattalin arzikin kasar ke ƙara taɓarɓarewa

Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kuma cocin Methodist na Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen yin addu’a domin al’ummominsu, ƙasar, da shugabanninta.
Da yake magana a taron cika shekaru 40 na cocin na Abuja Archdiocese na cocin Methodist, Tinubu ya bayyana cewa addu’a tana zama tushen ƙarfin zuciya da jagora, musamman yayin da ƙasar ke tafiya cikin ƙalubalen jagoranci mai wuyar sha’ani.
“Ina roƙonku da ku ci gaba da yin addu’a ba kawai don al’ummominku ba, har da ƙasar da muke ƙauna Najeriya da shugabanninta. Addu’o’inku suna zama tushen ƙarfin zuciya da jagoranci yayin da muke fuskantar ƙalubalen mulki,” in ji Tinubu.
Shugaban ya kuma ƙarfafa wa cocin gwiwa da ta ci gaba da ayyukanta na hidima da tausayi ga al’umma.
Ya kuma maimaita bukatar hadin kai wajen tunkarar matsalolin da Najeriya ke fuskanta.
Shugaban na Najeriya ya kara da cewa, “Kalubalen da muke fuskanta a matsayin ƙasa suna buƙatar haɗin kai. Coccinku na iya zama dandali na sauyi a zamantakewa, inda mutane za su haɗu don kawo sauyi, inganta zaman lafiya, da ɗaga darajar mutane.”
Tinubu ya kuma yaba wa gudunmawar cocin Methodist wajen gina ƙasa ta hanyar adalci, ilimi, da ayyukan jinƙai.
Ya ƙara jinjina wa rawar da cocin ke takawa wajen inganta zaman lafiya da haɗin kai a Najeriya, tare da ƙarfafa tattaunawa tsakanin al’umma daban-daban, da kuma ƙarfafa haɗin kai don aiki tare wajen cimma buri na bai daya.
Wasu daga cikin fitattun mutane da suka halarci taron sun haɗa da tsohon Shugaban Ƙasa Janar Yakubu Gowon, tsoffin Shugabanni Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio.
Babban limamin cocin Methodist na Najeriya, Mai Alfarma Oliver Ali Aba, ya kuma yi kira ga jama’a da su goyi bayan gwamnatin ta Tinubu.