October 18, 2025

Tinubu Ya Isa Saudiyya Domin Halartar Taron Ƙasashen Larabawa Da Na Musulmi

IMG-20241110-WA0020.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Shugaba Tinubu ya isa birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya domin halartar taron haɗin-gwiwa tsakanin kasashen Larabawa da na Musulmi

Jirgin da ya ɗauki shugaban ƙasar ya sauka ne a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ƙarfe 10:00 na safiya.

Shugaba Tinubu ya je Saudiyya ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, domin halartar taron da zai mayar da hankali kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.

Idan dai za a iya tunawa, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mista Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, shugaba Tinubu zai yi jawabi kan rikicin Isra’ila da Falasdinu yayin da ya jaddada kiran da Najeriya ta yi na a tsagaita buɗe wuta cikin gaggawa da kuma buƙatar gaggawan warware rikicin don tabbatar da  sulhu da zaman lafiya a yankin.

Har ila yau, Inanugan ya bayyana cewa, Najeriya ma za ta ba da shawarar sake yin wani sabon yunƙuri na farfado da tsarin ƙasa biyu a matsayin hanyar samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

A ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba 2024 ne za a fara taron haɗin-gwiwar tsakanin ƙasashen Larabawa da na Musulmi, kuma birnin Saudiyya zai karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashen duniya da dama da za su halarci taron.

Manyan jami’an gwamnatin Najeriya da suka haɗa da ministan harkokin waje Ambasada Yusuf Tuggar ne suka raka shugaban kasa taron.

Sauran ‘yan tawagar da suka raka shugaban sun haɗa da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu;  Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Alhaji Mohammed Idris;  da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Mohammed Mohammed.

Bayan kammala taron, shugaba Tinubu zai komo Abuja ne kamar yadda ake sa rai.