October 18, 2025

Sojojin Najeriya sun kama ƴanta’adda 3 da mai kai wa ƴanbindiga kayayyakin aiki a Taraba

FB_IMG_1728560767892.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Dakarun Runduna ta 6 na Sojojin Najeriya da na Sashen 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) sun kama wasu mutum uku da ake zargi ƴan bindiga ne da kuma wani mai kaiwa ƴan ta’adda kayayyakin aiki a Jihar Taraba.

Wadanda ake zargin da aka kama sun haɗa da Adamu Abubakar, Mohammed Bello, da Musa Adamu.

An kama su ne a garin Jeb-Jeb, wani yanki da ke kan iyakar Taraba da Jihar Filato, bayan samun sahihan bayanan sirri.

A cewar masanin tsaro Zagazola, waɗannan mutane suna da hannu a wasu munanan laifuka da suka haɗa da fashi da makami, garkuwa da mutane, da kuma hare-haren tashin hankali kan al’umma a yankin.

Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Runduna ta 6, Kyaftin Olubodunde Oni, ya tabbatar da kamen, inda ya ce “an gudanar da wani shiri na musamman a ranar 7 ga Oktoba 2024 a yankin Andamin na ƙaramar hukumar Karim Lamido, wanda ya kai ga nasarar cafke wasu da ake zargin ƴan bindiga ne”.

Haka nan kuma, an kama wani ƙasurgumin mai kai wa ‘yanta’adda kayayyakin aiki, Musa Inusa, a garin Bunka na ƙaramar hukumar Lau.

Kayayyakin da aka kwace daga hannunsa sun haɗa da wuƙa, ƙwayoyi masu haɗari, da kuma wasu fakitin tabar wiwi da ake zargin ya mallaka.

Runduna ta 6 ta Sojojin Najeriya ta tabbatar wa jama’a cewa za su ci gaba da yakar ƴan bindiga da ƴanta’adda da ƙarfi.

Sannan rundunar sojin ta yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da faɗakar da hukumomin tsaro idan sun ga wani baƙon abu.

1 thought on “Sojojin Najeriya sun kama ƴanta’adda 3 da mai kai wa ƴanbindiga kayayyakin aiki a Taraba

Comments are closed.