Malaman makaranta a Taraba sun shiga yajin aiki saboda kisar abokin aikinsu
Daga Sabiu Abdullahi
Kungiyar Malaman Makarantun Sakandare ta Jihar Taraba ta umarci mambobinta da su dakatar da harkokin karatu har sai an ba su umurni da su ci gaba.
Hakan ya biyo bayan kashe daya daga cikinsu mai suna Bassey Sardauna, malamin makarantar Model Government Day Secondary School da wasu tsaffin daliban makarantar suka yi.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Sule Abasu ya fitar, ya ce ba za su koma aiki ba har sai an bi wa dan ƙungiyarsu hakkinsa.
“Yan’uwa, a wani abin bakin ciki mun samu mummunan labari na rasuwar abokin aikinmu, wanda aka kashe shi da wuƙa.
“Wannan wani abu ne marar daɗi ji da aka yi mana.
“An san malamai da gudummawar da suke bayarwa wajen ci gaban al’ummarmu.
“Ku lura cewa rauni ga ɗaya, rauni ne a gare mu duka.
“Muna nan muna nuna ɓacin ranmu game da wannan mugun aiki ”
Wata sanarwa da kwamishinan ilimi na jihar, Augustina Godwin ya fitar ta ce an kama wasu da ake zargi tare da fara bincike.
Gwamnati ta yi alƙawarin inganta tsaro a makarantu ta hanyar tura jami’an tsaro da makamai da kuma wadanda ba sa dauke da makamai domin kauce wa ci gaba da kai hare-hare irin waɗannan.



